Masu sa ido na kasashen duniya da na cikin gida, sun yi Allah wadai da kama wani dan jarida, dan kasar Pakistan, saboda ya bayar da rahoto game da zanga-zangar 'yan gwagwarmaya da aka ce suna da alaka da wata kungiya mai kare hakkokin kabilun Pashtun na kasar.
An kama Gohar Wazir, wanda ke aiki a wani gidan talabijin mai zaman kansa wanda ake kira Khyber News sannan yana da manhajar tashar YouTube tasa na kansa, tare da wasu mutane 21 a farkon wannan makon akan zargin su da neman ta da hankalin jama’a.
Cibiyar kare hakkin 'yan jaridar da ke nan Amurka wato (CPJ) a takaice, ta yi gargadin cewa hana 'yan jaridu gudanar da ayyukkansu na watsa labarai, zai yi aibi ga "tsarin mulkin demokradiya a Pakistan", don haka cibiyar ta bukaci da a hanzarta sakin dan jarida cikin gaggawa.