Wani malamin makarantar sakandare ya gano dabarar amfani da waka da rawa, wajen cusa ma matasa sha’awar darasin lissafi, abin da ya taimaka sosai wajen fahimtar da su ke wa darasin na lissafi. A baya dai wani mai ilimin lissafi mai suna Dr. Dikeoha Okwu da ke birnin Enugu, ya kirkiro irin wannan dabarar, wace ya sa wa suna Dikeohamatics, to amma sai ya kasa samun goyon baya daga takwarorinsa da kuma hukumomin Najeriya.
To ana nan sai wani malamin lissafi a makaranatar sakandare ta Loral International Boarding School da ke Igbesa Jahar Ogun, mai suna Mr. Anyanwu Emmanuel Obiaha, ya bullo da irin wannan salo na saukaka koyar da lissafi da kuma fahimtarsa, cikin walwala da nishadi irin waka da rawa, wanda ya sa daliban su ka cicci lambobin yabo ga makarantar.
Hasali ma, sakamakon jarabawar WASSCE dinsu ta 2014 ya ba da mamaki matuka. To ko wace shawara kwararru za su bayar ga malamai da iyaye da kuma dalibai game da bullo da irin wadannan dabarun? Wannan tambaya ce da watakila kwararru za su yi takaddama akai.
Your browser doesn’t support HTML5