An Kirkiro Manhajar Da Zata Magance Nacin Amfani Da Wayar Hannu

Jama’a da dama sun yi kokarin takaita amfani da wayoyin su hanu saboda kokarin kawar da nachin son amfani ko duba waya a koda yaushe,

Toh amma watakila samun nasarar kawar da nachin son anfani da wayar hannu a kowane lokaci na iya kasancewa ta hanyar amfani da wata sabuwar manhajar da aka kirkiro da zata ba mai amfani da waya lada ga duk wanda ya ajiye ko kyle wayarsa har na zuwa wani lokaci.

Sabuwar manhajar da akai wa lakabi da suna ‘’HOLD’’ zata iya gano lokacin da mutum yayi amfani da wayar sa, kuma zata baiwa dalibai lada ta hanyar la’akari da tsawon lokacin da dalibi ya ajiye wayarsa batare da yayi amfani da ita ba wajen duba facebook ko aika sako ta whatsapp.

Bayan mutum ya sanya manhajar a wayar sa ta sadarwa, sai mtum ya bar wayar zuwa wani tsawon lokaci batare da yayi amfani da wayar ba domin samun lada da za’a iya musayar ta da rabin farashin tikitin gidan kallon finafinai wato cinema, ko yin sayayya a farashi mai rahusa.

Dalibai na samun lada 10 a duk lokacin da basu yi amfani da wayar su ba har tsawon mintina 20, amma dalibi na bukatar addreshin aiki sako ta email domin karbar ladan da ya samu.

Yanzu haka manhajar ta fara aiki a birtaniya da zummar taimakawa dalibai wajen fanin ilimi ko karatu a ‘yan shekarun nan, saboda da damuwar yawan nachewa wayar sadarwa ta hanu da matsalolin da take da shi.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kirkiro Manhajar Da Zata Magance Nacin Amfani Da Wayar Hannu