Hukumar da ke hukunta manyan laifuka ta FBI a Amurka, ta ce satar fasaha na kara haifar da damuwa tare da zama babbar barazana.
Wannan ce matsayar da wasu mahalarta wani taro daga sassan duniya suka bayyana a wani taro da aka gudanar a birnin Las Vegas.
David Eagleman, na daya daga cikin mutane sama da 175,000 da suka halarci taron baje kolin Fasahar Zamani na kayayyakin laturoni wanda aka gudanar a wannan taro.
Shi malamin kwakwalwa ne a jami’ar Stanford ‘Neuroscientist’ a turance, wanda ya haɗu da wani kamfani wanda ke ƙirƙirar agogon hannu ‘Wristband’ yana kuma taimakawa mutane jin wasu bayanai ta hanyar fatar jikinsu.
An samar da na'urar ne bayan kwashe shekaru ana bincike, don haka Eagleman yana da burin ganin wannan nau’rar ta samu duk kariyar da ta dace a idon duniya.
Agogon dai zai dinga nadar bayanai daga fatar mutum, yana kuma fassara bayanan don wasu su iya fahimtar me mutum ke nufi, ba tare da ya furta ko motsa wani sassan jikinsa ba.
Fatar jikin mutum na iya shaida abin da kwakwalwa ke son yi, ko tunani a kowane lokaci.
"Muna da duk kayan fasahar da suka kamata a ce muna da su, saboda haka, ba mu damu matuka game da satar fasaha ba. A gefe guda, wannan rukuni ne na mutane dubu 170, saboda haka wani abu ne da ya kamata mu lura da shi," in ji Eagleman.