Masana fasahar zamani, sun kirkiri wani na'urar sanyaya kayan abinci ko kuma firij, wanda zai rika yin wasu ayyuka da firij din da aka saba amfani da shi ba ya yi.
Abu kawai da kake bukata shi ne ka faɗa wa firij ɗinka irin nau’ukan abincin da kake son ka dinga ci a ko da yaushe.
Firij din zai shirya maka girke-girke na tsawon mako mai zuwa, ya kuma aika jerin sayayyar zuwa wayoyinka lokacin da ya lura da cewar nau’ukan abincin da kake so suna shirin karewa.
Kyamarar ko na'urar daukan hoto da ke cikin rishon dafa abinci ta kan nuna wa mutum yadda abincin yake dahuwa har ma da daura abinci a shafin Instagram.
Waɗannan su ne wasu sabbin kayan fasahar "smart kitchen" da aka nuna a wannan makon a taron baje-kolin kayan fasahar zamani da aka gudanar a birnin Las Vegas da ke nan Amurka.
An yi gasar don nuna sabbin kayan aikin dafe-dafe, wanda suke fatan za su iya tafiya da zamani.
Kayatattun kayan na zamanin da aka baje na dauke da na’urorin da suke tafiya da karni na 21, manyan kamfaninonin da ke samar da kayan aiki kamar Samsung, LG Electronics da sauransu.