An Killace Kashi Daya Cikin Hudu Na Al'ummar Italiya

A yau Litinin kasar China ta bayar da sanarwar samun adadin sabbin mutane mafi karanci, da suka kamu da cutar Coronavirus, yayin da a kasar Italiya kuwa kashi daya cikin hudu na kasar aka killace, kana fasinjoji dake cikin wani jirgin shakatawa na shirin barin jirgin a jihar California ta Amurka, bayan an samu wasun su da cutar.

Hukumomin lafiya a China sun ce an samu karin mutum 40 da suka kamu da cutar, wannan shi ne mafi karanci da aka samu tun daga watan Janairu, kafin gwamnati ta saka takunkumi a kan tafiye-tafiye da taruwar jama’a a wasu yankunan da cutar tai kamari.

Italiya dai ta fara killace mutane daga yankin ta na Arewacin kasar, wanda ya hada da yankin jihohin Milan da Venice. An samu karuwar mace-mace a jiya Lahadi da da 133 da ya kai adadin wadanda suka rasu 366.