A ranar Laraba 1 ga watan Afirilu, babban Hafsan Hafsoshin sojin Najeriya Lt. Janar Tukur Yusuf Buratai ya kaddamar da wasu motocin yaki wadanda aka kera a Najeriya guda 7 ga rundunar sojin Najeriya, don samun ci gaba a fafatawar da suke yi da kungiyar mayakan Boko Haram.
An kera motocin ne a karkashin jagorancin kwamandan dake kula da shiyyar arewa maso gabashin Najeriya Manjo Janar Olusegun Adeniyi, don rage kudaden da ake kashewa wajen sayo motocin da ake yaki dasu.
Babban Hafsan Hafsoshin sojin Najeriya Lt. Janar Tukur Yusuf Buratai, wanda Manjo Janar Olusegun Adeniyi ya wakilta a taron kaddamarwar, ya ce tun a watan Agustan shekarar 2019 suka soma binciken bunkasa al’amuran kimiyya da kayayyakin yaki na jami’an soja, kuma a yanzu haka sun samu nasarar maida motocin yaki masu sulke zuwa motocin yaki na zamani.
Sannan ya kara da cewa za a samu rangwamen kashi 7 cikin 100 na kudin da ake amfani dasu wajen sayo motocin a kasashen waje.
Adeniyi ya kuma ce motocin da aka kera, bom baya ratsa su. Motoci ne masu ingancin gaske kuma zasu iya jure wa duk wani hari, a cewarsa.
Saurari karin bayani cikin sauti daga Haruna Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5