An Kawo Karshen Mutuwar Jakuna Da Dawakai A Nijar

Yanzu haka ana iya cewa, hukumomin kiwon lafiyar dabbobi a Jamhuriyar Nijar, sun gano cututtuka dake sanadin mutuwar jakuna da dawaki, da a ke kira Glume. Shugaban ma'aikatar kiwon lafiyar dabbobi ta Birni N'Konni Ibrahim Gadaje, yayi muna karin bayani.

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da a ke iya cewa, bayan da dama daga cikin jakuna da ma dawakai sun mutu sanadiyar kamuwa da wannan cutar mai suna Glume, wadda a ka gano maganinta bayan biciken da hukumomin kasar suka yi, haka da irin magungunan da ya kamata ayi amfani da su domin tunkarar cutar.

Daya daga cikin garuruwan da suka yi fama da wannan matsalar shine, Massalata a cikin da'ira Birnin Konni da ke jihar Tahoua. Hakimin garin Dagel Ibro Dan-Aman, yayi murna da gano cutar, inda yake cewa lale marhaban.

Suma mazauna karkarar wanda jakuna da dawakan su ke taimaka musu wajan yin ayukan yau da kullun, sun yi marhabin da gano cutar. Kuma suna kira ga hukumomin kasar da su taimaka musu wajen kawo karshen wannan annobar.

Ga rahoton Harouna Mamane Bako daga Jamhuriyar Nijar.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kawo Karshen Mutuwar Jakuna Da Dawakai A Nijar 2'30"