Ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar Afghanistan ta tabbatar da cewa anzo karshen mamayewar da aka yi wa ofishin jakadancin Iraq dake Kabul bayan kimanin sa’aoi hudu.
Ma'aikatar tace, jami’an tsaron kasar Afghanistan sun bindige mahara uku, kuma dan sanda daya ne kawai aka jiwa rauni a musayar wutar,babu kuma wani ma’aikacin ofishin jakadancin da aka jiwa rauni.
‘Yan bindiga hudu dauke da makamai ne suka kutsa ofishin jakadancin Iraq dake babban birnin kasar Afghanistan yau Litinin.
Kungiyar IS ta kafar Kamfaninta na yada labarai ta Amaq ta dauki alhakin kai harin.
Ma’aikatar harkokin cikin gidan Afghanistan tace daya daga cikin maharan ya tarwatsa kansa a kofar shiga harabar ofishin jakadancin, abinda ya bada dama ga sauran maharani su shiga harabar ofishin.
Hare haren da mayaka ke kaiwa a Kabul sun yi sanadiyar asarar rayukan farin kaya da dama cikin wannan shekarar.