An Kauracewa Taron Addu'o'in Ban-Kwana Da Marigayi Mugabe

Dakarun Zimbabwe zagaye da gawar marigayi Robert Mugabe

Rahotanni daga Zimambwe na cewa mutane kalilan ne suka halarci wajen taron ban-kwana da gawar tsohon shugaban kasar Robert Mugabe, wanda aka yi a filin wasanni a Harare.

Bayanai sun yi nuni da cewa kashi daya cikin uku na Filin wasa masu halartar taron suka cika - filin da ke daukan mutum dubu-sittin.

Shaidu sun bayyana cewa taron bai yi armashi ba ko kadan, idan aka kwatanta da dumbin mutanen da suka cika filin wasan makil, a lokacin da za a rantsar da shugaban kasar da ya gaje shi.

Na gwammace na je na yi wani abu, kamar na zauna a gida na huta cikin iyalina,” maimakon zuwa taron." Inji Happy Marufu, dan kasar ta Zimbabwe.