An Kashe 'Yan Okada Ashirin A Jihar Kebbi

A jihar Kebbi kimanin ‘yan Okada, ashirin ne suka rasa rayukansu a hannun barayi a jihar a cikin watani shida.

Shugaban kungiyar masu haya da Okada, na jihar ta Kebbi, Malam Nafi’u Zaki, ne ya bayanawa kamfanin dillanci labarai na Najeriya, a birnin Kebbi babban birinin jihar, ya kara da cewa kashe kashen sun faru ne a ciki kananar hukumomi ukku ne.

Shugaban yace a cikin wadanda suka mutu mutane goma sha daya sun fito daga Birnin Kebbi ne, mutane tar da suka rage sun fito daga Argungu da Yawuri ne.

Yace kimani ‘yan kungiyar dari takwas ne suka ajiye aiki haya da Babur domin gudun kada a raba su da abin neman abincinsu.

Shugaban ‘yan Okadan Nafi’u Zaki, yayi kira ga gwamnati jihar da hukumomin tsaro dasu kawo wa kungiyar dauki, yana mai cewa sana’ar tana taimakawa wajan rage zaman kashe wando.