Wasu mutane dauke da bindigogi sun fafari lauyan babban dan adawar jam’iyyar siyasa a kasar Mozambique tare da wani babban jami’in jam’iyyar sannan anyi musu mumunan harbin da ya kashe su a motar su a babban birnin kasar a cewar jam’iyyar su a ranar asabar.
Yayin da kasar take dakon sakamakon zaben dake cike da rashin tabbas wanda ya sa ake dada zargin cewa anyi aringizon kuri’u a zaben sannan gwamnatin da ta dade tana mulki a kasar tana kame wadanda suke bayyana ra’ayoyin da suka saba nata.
Jam’iyyar PODEMOS mai adawa ta ce an kashe Elvino Dias, wani lauya da mashawarcin dan takarar shugaban kasar jam’iyyar Venancio Mondlane da kakakin jam’iyyar bayan da wasu masu bindiga cikin wasu motoci 2 suka budewa motar da suke ciki wuta akan babban titin birnin Maputo da daren Jumma,a.