An kashe wani mutumin da ya kaiwa yan sanda hari a Paris

PARIS POLICE ATTACK

Babu wanda yaji rauni a harin da jami’ai suka ce da gangan ya kaishi.

Rahotannin farko na nuni da cewa, hukumomi sun san da zaman mutumin dan shekaru talatin da daya da aka sani da tsats-tsauran ra’ayi.

Tawagar jami’an tsaro dake da kwarewa kan warware bom ta killace wurin, bisa ga cewar kakakin ma’aikatar harkokin cikin gida. ‘yan sanda sun ce an sami karamar bindigar hannu, da bindigogin da ake sabawa a kafada, da kwalaben man fetir a cikin motar.

Mai shigar da kara kan ayyukan dakile harin ta’addanci na kasar Faransa ya fara gudanar da bincike kan lamarin.