An Kashe Wani Dan Majalisa da Aka yi Garkuwa da Shi A Jihar Taraba

Yan Sandan Najeriya

Yan Sandan jihar Taraba dake Arewa-maso-gabashin Najeriya sun tabbatar a jiya Litinin cewa dan majalisar dokokin jihar da ya fada hannun masu garkuwa da mutane, Mr. Hosea Ibi y amutu.

Fiye da wata guda ke nan da masu garkuwa da mutane suka sace wannan dan majalisar dokokin yayin da ya ziyarci mahaifiyasa kuma tun daga wancan lokacin ne ake ta fafutukar ganin an ceto shi, to amma hakarsu bata cimma ruwa ba.

Tun da farko masu garkuwan sun nemi a basu kudin fansa na Naira miliyan dari, kamar yadda wata majiya ta tabbatar.

Rundunan yan sandan jihar Taraban, ta bakin kakakinta ASP David Misal, tace an gano gawar dan majalisar ne a wani kauye dake hanyar Kashimbila, wanda kuma kawo yanzu ba wanda aka kama dangane da kisan.

Yanzu haka dai wannan batu ya jefa al’ummar mazabar dan majalisar wato Takum One da ma jihar Taraban cikin wani yanayi na zullumi. Hon. Emmanuel Bello, tsohon kwamishinan yada labarai ne a jihar kuma dan yankin da dan majalisar da aka kashen ya fito, ya bayyana halin da suka tsinci kansu a yankin.

Yanzu haka dai a Najeriya satar mutane domin neman kudin fansa na neman gagaran kundila, yayin da a kullum kuma hukumomin tsaro ke cewa suna nasu kokari wajen maganace lamarin.

Ga ratohon da wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdulaziz ya aiko mana kan wannan:

Your browser doesn’t support HTML5

ABDUCTED LAW MAKER