An kashe wadansu 'yan siyasa biyu a Jihar Plato

Wadansu mahara a Najeriya

An kashe wadansu ‘yan siyasa biyu a Najeriya jiya lahadi yayinda suke halartar jana’izar bai daya, ta wadanda aka kashe a wani hari ranar asabar.

An kashe wadansu ‘yan siyasa biyu a Najeriya jiya lahadi yayinda suke halartar jana’izar bai daya, ta wadanda aka kashe a wani hari ranar asabar.

Jami’ai sun ce saneta Gyang Dantong mai wakiltar mazabar Jos ta arewa, da shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Plateau Gyang Fulani, na cikin sama da mutane ishirin da aka kashe a wajen jana’izar kusa da Jos babban birnin jihar Plateau. Yayinda dan siyasa daya ya tsallake rijiya da baya.

‘Yan majalisar duka ‘yan kabilar Berom ne, Jami’ai sun dorawa Fulani makiyaya alhakin harin. Shugabannin al’ummar Fulani sun musanta cewa, suna da hannu a harin na jiya lahadi.

Da asubahin ranar asabar, wasu mahara dauke da makamai suka kai hari kan wadansu kauyuka biyu a kusa da Jos, suka kashe mutane kimanin 50 da suka hada da wadansu jami’an tsaro da suka yi musayar wuta da maharan.