An Kashe Shugaban Wata Kungiyar 'Yan Tawaye a Syria

Syria

Bam da ya tarwatse ya hallaka Hassan Aboud shugaban wata kungiyar 'yan tawaye tare da wasu kwamandojinsa yayin da suke taro a wani gida. Har yanzu kungiyar na fafatawa da dakarun Bashir Al-Asasad shugaban a cikin Syria.

A Syria an kashe Hassan Aboud shugaban wata kungiyar ‘yan tawaye da wasu mutane 12 jiya talata.

Kungiyar da yake yiwa shugabanci da ake kira Ahrar al-sham ta tabbatar ta wani sakon da ta buga a shafin internet cewa shugaban nata ya halaka ne sakamakon wata fashewar bam a lardin Idlib. Ba tabbatas kan wadda yake da alhakin haddasa fashewar bam din, a yayinda kungiyoyin ‘yan tawayen kasar da suka karkasu, har yanzu wasu suna ci gaba da fafatawa da dakarun gwamnatin a sassan kasar da dama.

Wata kungiyar rajin kare hakin Bil’Adama tace bam ya tashi ne lokacinda Aboud da wasu kwamandoji suka hallara a wani gida domin suyi taro.

Kamar yadda kungiyar rajin kare hakkin Bil’Adama ta Syria mai cibiya a Ingila wacce take tara alkaluman mace macen da aka yi a yakin basarar da ake yi a Syria, tace akalla mutane 28 ne aka kashe a taron.

Kungiyar Ahrar-al-sham ta juma tana gwabzawa da kungiyar ISIS wacce ta kama yankunan kasashen Syria da Iraqi.