Sama da mutane hamsin aka kashe a jihar Oromiya ta kasar Ethiopia a loakcin da yan sanda suka sake hayaki mai sa hawaye da harbin gardi don tarwatsa masu zanga zangar kin jinin gwamnati a wurin wani bukin addini.
Hayakin mai sa hawayaen ya yi sanaidiyar turmutsutsu a jiya Lahadi. Jami’ai a kasar sun bada sanarawar cewa mutane 52 ne aka kashe.
Gwamnati tace mutane da dama ne suka jikata a wannan tarzomar da ta tashi a wurin bukin shekara inda kabilar Oromo ke shagalin kawo karshen damana.
Dubban mutane ne suka taru a gabar kogin Harsadi don yi bukin godiya ta shekara a garin Bishoftu mai tazarar kilomita 40 daga babban birnin kasar Addis Ababa.
An taba samun makamanciyar wannan gagarumar zanga zanga a Oromiya shekaru biyu da suka wuce, da farko takaddama a kan fili ne ya janoyta.
Mutane da yawa sun sha rasa rayukkansu a irin wadanan tashe-tashen hakullan a kasar ta Ethiopia daga shekarar 2015 zuwa yanzu.