Jami’an kasar Pakistan sunce wasu yan bindiga a birnin Karachi dake kudancin kasar sunyi wa wata bas dake jigilar yan sanda na musamman kwantar bauna, suka kashe akalla jami’a hudu da raunana fiye da mutum talatin. Hukumomi sunce yan sanda suna sanye da kayan farar hula ne a lokacinda aka kaiwa bas dinsu hari jiya juma’a da dare a gundumar Korangi.
A wani wuri dabam kuma, wani mai harin kunar bakin wake ya kai hari Masalaci a arewa maso yammaci kasar ya kashe akalla mutane arba’in da takwas.
An kai wannan harin ne a yayinda fiye da mutane dari uku suka cika wani Masalaci domin yin salar juma’a a Jamrud baban birnin yankin Kyber. Hukumomi sunce akalla mutane dari ne suka ji rauni a wannan hari da aka kai ana tsakiyar yin azumin watan Ramadan.
Gidan talibijin ya nuna hoton vidiyon gine gine da aka lalata, gashi kuma a cikin Masalaci ana ganin rigunan da takalman mutane a warwatse a ko ina.
Sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton tayi Allah wadai da wannan kisa data ce anyi a lokacinda Musulmi a duk duniya suke azumi a wannan wata mai alfarma. Baban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya kofi Annan yace wannan hari da aka kai da gangan a wurin ibada ya bashi tsoro, ya kuma yiwa iyalin wadanda suka mutane ta’aziya da jaje ga yalan wadanda suka jikatta.
Babu dai kungiyar data yi ikirarin cewa ita keda alhakin kai wannan hari, to amma, a baya kungiyar Taliban a Pakistan ta kai irin wadannan hare hare domin ramuwar gaiyar kisan Osama bin Laden da Amirka ta yi.