An Kashe Mutane Da Dama A Farmakin Garin Daura

Wani yaro yana tsaye kan motar 'yan sanda aka kona lokacin wani hari kan caji ofis na Sheka a Birnin Kano, 25 Janairu 2012

Kwamishinan 'yan sanda yace an kashe mahara akalla su 4, yayin da wasu mazauna garin Daura a Jihar Katsina suke fadin cewa an kashe jami'an tsaro akalla 3.
Jiya alhamis cikin dare ne wasu mahara dauke da manyan bindigogi suka kai farmaki a kan bankuna, da ofisoshin 'yan sanda da wasu sassan garin Daura dake Jihar Katsina, inda aka shafe kusan tsawon dare ana musanyar wuta a tsakaninsu da dakarun gwamnati.

Kararrakin fashe-fashen nakiyoyi da harbe-harbe, sun firgita mazauna garin, wadanda wasu suka fake cikin gidajensu, wasu kuma suka fantsama daji domin gujewa abubuwan da suke faruwa.

Kwamishinan 'yan sandan Jihar Katsina, Abdullahi Magaji, ya ziyarci garin na Daura a yau jumma'a, inda ya dora laifin wannan farmakin a kan 'yan fashi. Yace jami'an tsaro sun samu nasarar harbe 4 ko 5 cikin maharan, a bayan da suka harbe wani direbansu, kuma ya kasa tuka motar da yake ja.

Kwamishinan 'yan sandan yace ba ya da masaniya game da kashe 'yan sanda ko sojoji, amma wasu mazauna garin na Daura sun fadawa wakilin sashen Hausa, Murtala Fauk Sanyinna, cewa sun ga gawarwakin wasu sojoji akalla 3, da wasu fararen hula su akalla biyu, a bayan da aka kammala fadan na Daura.

Ga bayanin Kwamishinan 'Yan sandan Jihar katsina da na mutanen garin Daura kan wannan farmakin.

Your browser doesn’t support HTML5

Bayanin Abubuwan Da Suka Faru Game Da Hare-Hare A Garin Daura