An Kashe Mutane 54 A Wani Farmaki Ta Sama

Syria.

Wani farmaki ta sama ya kashe akalla mutane 54 ciki har da mayakan IS da kuma fararen hula 28 a gundumar gabashin Syria ta Deir Ezzor a cewar masu sa ido a kan take hakin bil adama.

Cibiyar da take sa ido a kan take hakin bil adama a yakin Syria dake zaune a Birtaniya ta Syrian Observatory, ta ce an kai wani hari a kan wata ma’aikatar yin 'kankara da yammacin jiya Alhamis a kusa da iyakar Iraki, yankin dake hannun IS, inda kuma fararen hula da mutane da dama ke zaune.

Cibiyar mai sa ido a kan take hakkin bil adamar, ta ce ba a iya gano wanda ya kai harin nan da nan ba, ko jirgin da ya kai harin ya taso ne daga Iraqi ne ko kuma jirgin rundunar hadin gwiwa da Amurka ke jagoranta ne.

Kamfanin dillancin labaran gwamnatin Syria na SANA, ya dora laifin kai harin a kan rundunar hadin gwiwa da Amurka ke jagoranta, yana mai cewar jirgin ya kashe akalla mutane 30 kana ya jikata wasu da dama.

Shi kuma kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fada cewa, rundunar hadin gwiwar, ta ce akwai yiwuwar ita kanta ko kawayenta sun kai hari a inda cibiyar Observatory din tace an aikata kashe kashen.