An Kashe Mutane 10 a Gwagwarmayar Kare Aikin Raba Kayan Agaji

  • Ibrahim Garba

Jirgin Kayan Abinci Na Farko Kenan a Birnin Mogadishu Na Somaliya

An bayar da rahoton kisan mutane a kalla 10 a Mogadishu, babban birnin Somaliya, a daidai

An bayar da rahoton kisan mutane a kalla 10 a Mogadishu, babban birnin Somaliya, a daidai lokacin da dakarun Kungiyar Tarayyar Afirka da na gwamnatin kasar ke kokarin kare aikin rarraba kayan abinci daga hare-haren mayakan sa kai.

Shaidu sun ce mace-macen sun auku ne a yayin wani kazamin fada a yau Alhamis – kwana guda bayan da Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta kai ton 14 na kayan abinci zuwa Mogadishu ta jirgin sama.

An bayar da rahoton raunata akalla mutane 30 a yayin da dakarun gwamnati da na AU ke fafatwa da mayakan sa kai masu alaka da kungiyar al-Shabab mai alaka da al-Qaida, wadda ta hana Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin duniya shigo da kayan agaji.

Shaidu sun ce dakarun gwamnati sun kwace kasuwar Suq Ba’ad da ke tsakiyar birnin Mogadishu, wadda ita ce kasuwa ta biyu a girma a babban birnin.

Wani mai magana da yawun dakarun tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, Lieutenant Colonel Paddy Ankunda, y ace dalilin wannan fafatawar shi ne a tabbatar da cewa kungiyoyin agaji za su iya gudanar da ayyukansu tare da rarraba kayan agaji ga ‘yan Somaliya da ke mutuwa da yunwa.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da rahoton cewa Somaliyawa akalla 100,000 ne su ka kaura zuwa Mogadishu kwanan nan don neman abin da za su ci su rayu da kuma ruwa.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa mutane miliyan 11 a can gabashin Afirka na bukatar taimakon gaggawa, a daidai lokacin da yankin ke fama da fari mafi muni cikin shekaru 6000.