An Kashe Mayakn Al-Shabab 189 A Wani Samame Da Aka Kai A Mabuyar Su

Dakarun UPDF

Jami’an kasar Somalia da dakarun kasar Uganda na UPDF sun yi ikirarin kashe mayakan al-Shabab 189 a yammacin ranar Juma’a da kuma safiyar jiya Asabar a wani farmaki da suka kai a kudancin Somalia.

Da ya ke magana da sashen Somalia na Muryar Amurka ta waya, gwamnan yankin Lower Shabelle Abdulkadir Mohamed Nur Siidi, ya ce sojojin Uganda da ke karkashin hadakar dakarun Afrika na AMISOM, sun kashe kusan mayakan al-Shabab 200 ta amfani da jirgin sama mai saukar ungulu na yaki.

Da ma da farko, mataimakin mai magana da yawun rundunar Uganda Laftanal Kanal Deo Akiki ya ce, sojojinsu sun kashe akalla mayakan al-Shabab 189 a wani farmaki da ya lalata wasu makamai da aka dana da kuma wasu ababen hawa a hare dabamdaban.

Gwamna Siidii ya ce hare-haren ta sama, da kuma wadanda dakarun hadin gwiwa suka kai ta kasa, a ranar Juma’a suka faru da kuma a safiyar jiya Asabar a wasu kauyuka da ke tsakanin gundumomin Qoryoley da Janaale a kudancin yankin Lower Shabelle da ke Somalia.

“An fatattaki ‘yan bindigan a mabuyar su a kauyukan Sigaale da Adimole da kuma Kayitoy, masu nisan kilomita 100 a kudu maso yammacin Mogadishu babban birnin Somalia,” inji Nur.

Wata sanarwa daga ma’aikatar sojin Uganda ta fada cewa, “an lalata kayan yakin soja masu dimbin yawa da ma wasu kaya da ‘yan ta’addan ke amfani da su, yayin da aka kai musu farmakin.

Sanarwar ta kara da cewa “dakarun UPDF na Uganda ta kuma lalata wani zaman tattaunawa da al-Shabab ke yi, inda ta raunata ‘yan ta’addan da dama a Donca-daafeedow, wanda ke nisan kilomita bakwai daga garin Janaale.”