An kashe mai kushewa kungiyar Boko Haram a Najeriya

An kashe mai kushewa kungiyar Boko Haram a Najeriya

Yan bindiga a arewacin Najeriya sun kashe wani malamin addinin Islama wanda ya kushewa kungiyar Boko Haram.

Yan bindiga a arewacin Najeriya sun kashe wani malamin addinin Musulunci wanda ya kushewa kungiyar musulmin nan mai tsatsa-tsauran ra’ayi Boko Haram. An kashe Bashir Mustapha jiya asabar da safe a gidanshi dake birnin Maiduguri. Yan sanda sun ce wadansu mutane biyu dauke da makamai dake tafiya kan babur, sun shiga gidan malamin jiya asabar da safe suka kashe shi da almajiransa. Hukumomin suna dorawa kungiyar Boko Haram alhakin harin. Malamin ya kushewa koyarwar kungiyar a wani shiri na Radio. Wannan harin da sauran hare hare sun sa fargaba a zukatan jama’a cewa, kungiyar Boko Haram tana neman dawowa bayan arangamar da aka zubar da jini da gwamnati tayi da kungiyar a watan Yuli shekara ta dubu biyu da tara. Sama da mutane dari bakwai aka kashe lokacin da kungiyar ta kaiwa ofisohin ‘yan sanda da gine ginen gwammati hari, abinda ya sa rundunar sojin Najeriya kai kazamin farmaki.