Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce an kashe wani likita da ke taimakawa wajen yaki da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, a lokacin wani hari da aka kai kan asibitin da ke gabashin kasar.
Wasu mayaka dauke da manyan makamai ne suka far wa asibitin, wanda ke Butembo, daya daga cikin yankunan da cutar da Ebola ta fi kamari, suka kashe Richard Mouzoko, dan asalin kasar Kamaru.
Sannan sun raunata, wani jami’in lafiya dan asalin kasar ta Congo tare da wani direba, a cewar wata sanarwa ta daban da wakilin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin duniya a kasar ta Congo ya fitar.
Wannan hari na asibitin, shi ne na baya-bayan nan da aka kai kan wata cibiya da ke kula da masu fama da cutar ta Ebola, a matsayin martanin ‘yan bindiga da ke nuna rashin yarda da ayyukan yaki da cutar ta Ebola da kasashen duniya ke yi.