An kai harin a rugayen Fulanin dake kauyukan Shafaran, Shawal, Gumara, Kikan da kuma Kadamti da yan kabilar Bachama ke da rinjaye inda aka kashe mutane 45 yawancinsu mata da yara.
Da yake tabbatar da aukuwan lamarin,kakakin rundunan yan sandan jihar Adamawa , SP Othman Abubakar, ya ce kawo yanzu sama da mutum 30 ne aka kashe,kuma akasarinsu mata da kananan yara ne.
Yanzu haka dai tuni wasu shugabanin hadakar kungiyar makiyayan Najeriya ta Miyetti Allah suka ziyarci yankin,domin ganin halin da ake ciki. Mafindi Umaru Danburam shugaban kungiyar a jihohin arewa maso gabas, wanda da shi aka gudanar da jana’izar wadanda aka kashen ya ce sun kadu da abun da suka gani tare kuma da yin kiran ga gwamnatin kasar da ta binciki lamarin don gano wadanda ke da hannu cikin kisan.
Tuni dai wata tawagar gwamnati karkashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar Adamawa ta ziyarci yankin don jajantawa makiyayan, tare da saba layar kamo wadanda ke da hannu.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5