Tawagar samar da zaman lafiya na MDD dake kasar Mali tace jamian ta 4 da sojan kasar Mali 1 aka hallaka a jiya jumaa a wasu hare-hare guda biyu da aka kai, kana mutane 21 ne suka samu rauni.
Farhan Haq mukaddashin mai Magana da yawun Sakataren MDD ya fada cewa, wannan harin ba shine na farko ba domin jamian sun samu nasarar kassara wani yunkurin harin da akayi kokarin kai musu, duk da yake dai jamiian wanzar da zaman lafiya sunyi hasarar rayukan su a yankin Manaka.
Haq yace sakataren na MDD Antionio Guteres yayi ALLAH waddarai da wannan harin.
Mai Magana da yawun Sakataren yace harin da ake kaiwa masu aikin wanzar da zaman lafiya wannan tamkar kwatankwacin laifin yaki ne a karkashin dokokin kasa da kasa kuma ana iya wa wanda aka samu da aikata wannan hukuncin yaki.
Kwamitin samar da zaman lafiya na MDD yace za a samar da wani sabon rundunar soja daga kasashen dake yankin Sahel, da suka hada da Mali,Niger,Bukina Faso,Murtania da Chad, domin su samar da zaman lafiya a yankin