An bindige madugun adawa da shugaban kasar Rasha kuma tsohon mataimakin firai ministan Boris Nemtsov jiya da dare a tsakiyar birnin Moscow.
Ma’aikatar cikin gida tace an harbe dan shekaru 55 da haihuwa, Nemtsov sau hudu daga cikin wata farar mota dake wucewa yayinda yake tafiya da kafa a kan kogin Moscow dake kusa da Kremlin.
‘Yan sanda sun ce Nemtsov yana tafiya ne da kafa tare da wata mace da ta ziyarce shi daga Ukraine, lokacin da aka bude mashi wuta amma bata ji rauni ba. ‘yan sanda suna yi mata tambayoyi.
Cibiyar dillancin labaran gwamnatin kasar Itar-Tass tace an shaidawa shugaba Vladimr Putin nan da nan game da kashe Nemtsov, kuma Kremlin zata jagoranci gudanar da bincike.
Kakakin Putin yace shugaban kasar yana ganin lamarin yana kama da kisan sojan haya, kuma zai iya tada liki yayinda kungiyoyin hamayya ke shirin gudanar da jerin gwano gobe lahadi.
Shugaban Amurka Barack Obama ya fitar da sanarwa yana allah wadai da kazamin kisan, ya kuma yi kira ga Rasha ta gudanar da bincike cikin sauri, na ba sani ba sabo.
Nemtsov shine mataimakin firai minista a shekarar alib dubu da dari tara da casa’in kuma masu kula da lamura da dama a lokacin sun yi harsashen cewa shine zai gaji shugaba Boris Yetsin.
Bayanda shugaba Yetsin ya zabi Vladimir Putin ya gaje shi, kafin zaben Mr. Putin a shekara ta dubu biyu, Nemtsov ya zamo daya daga cikin wadanda suka fi kushewa shugaba Putin, musamman tun da aka fara rikici a kasar Ukraine bara.