An Kashe Fam Biliyan 2.75 Akan 'Yan Wasan Kwallon Kafa

Shugaban FIFA Gianni Infantino

A wani bincike da hukumar kula da kwallon kafa ta duniya, (FIFA) tayi kan batun kudaden da aka kashe a bana, wajan saye da sayarwa na ‘yan wasan kwallon kafa na duniya.

Lisafi na nuni da cewar a bana an kashe zunzurutun kudi har fam Biliyan £2.75 kan saye da sayarwa.

Inda hukumar ta FIFA tace kungiyoyin kwallon kafa na Kasar Ingila, su sukafi kashe kudi a cikin jerin kasashe manya guda 5 da sukayi fece a nahiyar turai wajan wasan tamola,kasashen sune Ingila, Spain, Jamus, Italiya da Kasar Faransa.

Inda alkaluman lisafi ke nuni da cewar a bangaren Firimiya lig na kasar Ingila sun Kashe fiye da kashi uku na yawan kudin da aka saye ‘yan wasan wato £2.75bn.

Anyi kiyasin kungiyoyin na Ingila sun batar da fam biliyan £1bn, a bana wajan sayen ‘yan wasa kawai.

Sai bangaren La-Liga na kasar Spain da suka Kashe, fam miliyan £480, Bundesliga na Jamus, tana rufa mata baya da fam miliyan £391, Sai Italiya, da ta Kashe fam miliyan £382.

Sai kuma Ligue 1 na kasar Faransa, wace ita tafi sayen dan wasa da tsada a bana inda PSG ta sayo dan wasan gaba Neymar, daga kungiyar Kwallon kafa ta Barcelona, akan zunzurutun kudi har yuro miliyan €222, Wanda yanzu haka shine yafi kowani dan wasan tamola tsada, a bana.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kashe Fam Biliyan 2.75 Akan 'Yan Wasan Kwallon Kafa -3'30"