An kashe akalla mutane biyar a Mogadishu babban birnin Somalia

Wajen da aka kai hari a Mogadishu

A kalla mutane 5 aka hallaka tare da raunata wasu 13 a wata fashewar bam da kuma bude wuta a daidai shelkwatar ‘yansanda masu kula da zirga-zirgar motoci a gabashin Mogadishu babban birnin kasar Somalia.

Majiyoyin asibitoci da shaidu sun tabbatar da aukuwar lamarin, wanda tuni kuma ‘yan ta’addar Al-Shabaab suka dauki alhakin kai harin. Shedun sun ce sun ji wata gagarumar kara da kuma harbin bindiga a daidai mashigar shelkwatar.

Wacce ke kusa da ofishin jakadancin Dubai a lardin Shangani da ke kasar. Bam ya tashi ne daga wata mota da dan kunar bakin wake ya tuko zuwa wajen, daga bisani kuma wani dan ta’addar daban ya bullo yana kokarin shiga ginin shelkwatar.

Amma jami’an ‘yan sanda suka yi nasarar harbe shi har lahira, kamar yadda majiyoyi daga jami’an tsaron suka shaidawa Muryar Amurka. Suma ma’aikatan kwasar marasa lafiya sun fadi cewa matattu 5 suka kwasa da majinyata 13. Majiyar daga jami’an tace ‘yansanda 3 na cikin matattun.