An Kashe Akalla Mutane 18 A Fada Tsakanin Musulmi Da 'Yan Kabilu A India.

Wata 'ya mace take ciyar da kaninta abinci a wani muhalli da aka tsara sakamakon ambaliyar ruwa a India.

Fiyeda mutane dubu talatin ne suka gudu daga gidajensu a arewa maso gabashin India sakamakon barkewar fada tsakanin kabilu da suke yankin da kuma musulmi ‘yan kaka gida.

Fiyeda mutane dubu talatin ne suka gudu daga gidajensu a arewa maso gabashin India sakamakon barkewar fada tsakanin kabilu da suke yankin da kuma musulmi ‘yan kaka gida.

Jami’ai a jihar Assam sun fada yau litinin cewa an kashe akalla mutane goma sha takwas a ‘yan kwanakin nan, sabo da fada kan kan ‘yancin mallakar kasa.

New Delhi ta tura sojoji domin shawo kan rikicin, da kuma bude sansanonin ‘yan gudun hijira ga wadan da suka rasa muhallansu.

Anjuma ana fama da kiyayya da zarge zargen satar filaye a yankin, tsakanin ‘yan kabilar Bodo da dubban musulmi daga Bengali, wadanda da yawa yawnsu sun zo yankin ne daga gabshin Pakistan, kamin yankin ya balle ya zama kasar Bangladesh a 1971.