An Kara Yawan Yan Sandan Kwantar Da Tarzoma Da Sauran Jami’an Tsaro A Garin Bama

A ci gaba da shirin gwamnatin jihar Borno na sake gina garin Bama, da kuma mayar da mutanen garin a watan Janairun shekara mai zuwa, yanzu haka an ‘kara yawan ‘yan sandan kwantar da tarzoma da jami’an shige da fice na immigration da kuma jami’an tsaron farin kaya don ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro a cikin garin Bama.

Mukaddashin kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno, Mr. Wakili, shi ne ya mika rukunin jami’an tsaron ga gwamnan jihar a cikin garin Bama, domin su ci gaba da aikin sa ido kan abubuwan dake faruwa a yankin. Mr. Wakili yace “munzo ne domin mu taimakawa takwarorinmu jami’an soja, mu kuma mayar da harkokin fararen hula a garin Bama.

Bayan mika jami’an tsaron ga gwamnan jihar Borno, sai shima ya nuna godiyarsa da maraba da su, har ma yayi musu alkawarin ‘daukar nauyin abincin su da kuma biyansu albashi na watanni biyu biyu. Gwamnan yace zai ci gaba da zuwa garin Bama har sai ya tabbatar da cewa an gama sake gina garin a watan Disambar wannan shekara.

Saurari cikakken rahotan Haruna Dauda Biu.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kara Yawan Yan Sandan Kwantar Da Tarzoma Da Sauran Jami’an Tsaro A Garin Bama - 2'52"