An kara tsaurara matakan tsaro a jihar Neja, dake tarayyar Najeriya, hukumomin jihar dai sun ce sun dauki matakin tsaurara tsaron ne domin hana kwararan ‘yan kungiyar Boko Haram, dake san fatattaka daga rundunar Sojan Najeriya, a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Jihar Neja, dake yankin tsakiyar Najeriya, nada maya mayan dazuzzuka daka iya bada mafaka ga ‘yan kungiyar ta Boko Haram, da Sojojin Najeriya suka ce sun tarwatsasu dag dajin Sambisa.
Kakakin ‘yan Sandan jihar Neja, DSP Bala Elkana, yace akwai zaratan jam’an tsaro na hadin guiwa, sama da dubu daya da aka tura bakin dajin Kamuku daya hada jihohin Neja, da Kaduna.
Itama Gwamnatin jihar Nejan, ta fitar da wata sanarwar dake jan hankalin jama’a, akan sanya idanu ga bakin dake shiga jihar, sakataren labaran Gwamnan jihar Jibril Baba Ndaci, yace maganar tsaro ba abune na wasa ba saboda haka yasa Gwamna yayi riga kafi.
Matakan da Gwamnatin jihar Nejan dai ke dauka yana zuwa ne a dai dai lokacin da kungiyar ta Boko Haram ta fitar da wani sabon bidiyo dake nuna cewa kungiyar na nan daram a dajin Sambisa.
Your browser doesn’t support HTML5