An Kara Daukan Matakan Tsaro A Tsaunin Mambilan Taraba

Kwamishanan 'yan sandan jihar Taraba da yanzu yake tsaunin Mambila

Biyo bayan wani harin da aka sake kaiwa tsaunin Mambilan Taraba, wasu manyan jami'an tsaro da suka hada da kwamishanan 'yan sandan jihar sun tare a tsaunin da zummar tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Don maido da doka da oda,biyo bayan hare haren da ake kaiwa tsaunin Mambila a jihar Taraba arewa maso gabashin Najeriya,yanzu haka an tura karin jami’an tsaro tare da tura jirgin yaki mai saukar angulu.

A cewar mai magana da yawun 'yan sandan jihar da Muryar Amurka ta tuntuba, harin da aka sake kaiwa jiya ya yi sanadiyar tarewar kwamishanan 'yan sandan jihar tare da wasu manyan jami'an tsaro a tsaunin Mambilan domin dakile kara asarar rayuka.

Alkalumma na nuni da cewa kawo yanzu wajen rayuka goma ne suka salwanta amma an kama wasu da ake kyautata zaton suna da hannu a lamarin 'yan kwanakin nan tare da kara cafke wasu bakawi jiya da aka samesu da kwari da baka da adduna da dai wasu kayan fada.

Ibrahim Abdulaziz na da karin bayani a wannan rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kara Daukan Matakan Tsaro A Tsaunin Mambilan Taraba - 3' 14"