An kammala wunin farko na babban taron jam'iyar Republican ta Amurka

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyar Republican Mitt Romney da matarsa Ann

Gwamnan Jihar New Jersey a nan Amurka, Chris Christie, ya zargi jam’iyyar Democrat da laifin durkusar da Amurka, yana mai bayyana shirin jam’iyyar a matsayin na nuna tamkar komai na tafiya sumul yayin da take kara ingiza Amurka cikin wagegen rami na bashi.

Christie shi ne ya gabatar da babban jawabi daren jiya talata a a ranar farko ta babban taron tsayar da dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar Republican a birnin Tampa dake Jihar Florida.

Gwamna Christie yace, ban san ra’ayoyinku ba, amma ni dai ba na son ‘ya’ya da jikoki na su karanta yadda rayuwa take da dadi a karnin Amurka na farko a cikin wani littafin tarihi. Ba na son su gaji gwamnatin da ta fadada kanta, ta tabkawa jama’a haraji ta kashe kudaden har ma ta ciyo bashin da ya maida al’umma kamar ‘ya’yan bora. Ina son su rayu cikin karnin Amurka na biyu na gawurta.

A wannan rana da Mitt Romney ya tabbata a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar republican, Christie ya yaba masa a zaman mutumin da zai yi jagoranci bisa imani tare da fadawa Amurkawa gaskiyar da ake bukata don maido da kasar kan hanyar bunkasa.

Christie yayi magana ne jim kadan a bayan da mai dakin dan takarar, Ann Romney, ta nemi Amurkawa da su ba mijinta damar shugabancin Amurka zuwa ga turba mafi a’ala.

Ann Romney ta ce ba zan iya fada muku abubuwan da zasu iya faruwa cikin shekaru 4 dake tafe ba, amma na tsaya a gabanku yau din nan a matsayina na uwa, matar aure, kaka, kuma Ba Amurkiya ina yi muku alkawari guda: Wannan mutumi (Mitt Romney) ba zai kunyata ku ba.