Yayinda ya kasance a taron, shugaban Najeriya Muhammad Buhari, ya ce babu shakka miyagun kalamu da miyagun wa'azi da wasu malamai su keyi na gaba gaba wajen haddasa ta'addanci a nahiyar Afirka da ma duniya gaba daya.
A ganin shugaba Buhari wajibi ne a yi tsarin da zai tabbatar cewa malaman addini sun yi wa'azi na gaskiya da adalci domin kawar da tashe tshen hankula.
Ministan tsaron Najeriya Manjo Janar Mansu Dan Ali, wanda yake cikin tawagar shugaba Buhari, ya ce akwai wasu muhimman abubuwa da yakamata a yi domin a nuna cewa ta'addanci ba abu ba ne nagari. Ya yi misali da maganar wa'azi da juya tunanen mutane su zama masu tsatsauran ra'ayin addini, duk wadannan ya kamata a san yadda za'a dakilesu domin a samu kwanciyar hankali.
Akan abubuwan dake faruwa a cikin Najeriya da suka haddasa rikici ko zasu iya haddasa wasu kamar kashe shugaban Boko Haram na farko, Muhammad Yusuf tare da ci gaba da tsare shugaban kungiyar Shiya, wato Shaikh Ibrahim El-zakzaki, Janar Mansur Dan Ali ya ce suna cikin abubuwan da aka gano. Suna cikin rashin adalci da rashin gwamnati ta kwarai.
A taron an bukaci shugabannin su dinga yiwa mutanesu adalci kuma a Najeriya an kama hanyar yin hakan.
Dangane da maganar Yusuf Muhammad Janar Mansur ya ce har yanzu maganar tana gaban shari'a a kotu saboda haka ba zai iya ce komi a kai ba. Sai a bari sai an kai karshen shari'ar.
Ga rahoton Umar Fruk Musa da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5