Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ware sati guda, 24 zuwa 30 a watan Afrilun kowace shekara a matsayin satin rigakafi na duniya, lokacin da ake jaddada muhimmancin yin rigakafi.
An ware satin ne don karfafawa mutane gwiwa game da allurar rigakafi don kariya daga cutuka musamman masu yaduwa.
Taken satin rigakafi na duniya na bana shi ne Fatan Tsawon Rayuwa ga kowa domin kokarin hada kan al'umma wajen yin rigakafi, ta yadda za su cimma burinsu wanda ake tsammanin zai taimaka wajen kare 'yan uwansu tare da samar da ingantacciyar rayuwa
Haka kuma hukumar ta ware ranakun ne don ganin gwamnatoci sun bi dukkan hanyar da ta dace don samar da ingantattun rigakafi ga al’umma.
Har ila yau hukumar na kokarin ganin tabbatar da cewa a’lumma a duk fadin duniya sun samu kariya daga cututtuka masu yaduwa da zummar kawar da wasu daga cikin cututtukan kwata kwata.
Jami'i a Hukumar Lafiya Matakin Farko ta kasa bangaren bada agajin gaggawa na al'amuran polio, Dr. Usman Sa'idu Adamu ya ce rigakafi ya taimaka wajen kawar da cututtuka da dama a Najeriya.
A na shi bangaren, Dr. Lawal Musa Tahir, ya jaddada muhimmancin yin allurar rigakafi.
Na zanta da wasu ‘yan Najeriya don sanin ra’ayinsu game da allurar rigakafi, ga kuma sun bayyana cewa ya na da alfanu sosai.
Bincike ya nuna cewa rigakafi kan kare miliyoyin mutane daga kamuwa da cututtuka a kowacce shekara, kuma shi ne matakin farko da ke kare yaduwar cututtuka a tsakanin al’umma, wanda ya sa Hausawa kan ce rigakafi yafi magani.
Saurari rahoton Hausa Umar:
Your browser doesn’t support HTML5