Bayan kammala gasar motsa jikin Olympic ta masu fama da wata nakasa, wadda hadaddiyar daular laraba ta karbi bakuncin wasan na bana, kasar India, ita ce ta fi lashe lambar yabo a gasar, inda ta sami zinare 60, da azurfa 83, da kuma tagulla 90. Sai kuma mai masaukin bakin wato Hadaddiyar Daular Larabawa, wadda ta zo ta biyu da zinare 47, da azurfa 43 da kuma tagulla 54.
'Yan wasa 60 da suka wakilci tarayyar Najeriya a gasar, sun taka rawar gani wajen samun lambonin yabo na zinare da azurfa da kuma tagulla, bayan fafatawa a wasanni guda 8, da ta yi, da suka hada da kwallon tebur, gasar ninkaya, da kwallon kwando da kwallon kafa, da kuma tseren keke da sauran su.
Tawagar ‘yan wasan motsa jikin ta Najeriya sun samu lambobin yabo kamar haka, zinare 9, azurfa 7 da kuma tagulla 5.
A ranar 14 ga watan Maris na shekarar 2019 aka bude gasar wasannin motsa jikin ta masu fama da larurar nakasa ta duniya a birnin Abu Dhabi. Kasashe daban daban ne suka fafata a wasanni 24.
WASHINGTON D.C. —