A ranar juma’a taron kasashen duniya kan yanayi COPS 29 ya kai dare, bayan rubuta jadawalin daya haifar da cecekuce, da ya bukaci kasashen da suka cigaba su jagoranci samar da dala bilyan 250 a kowacce shekara, ya zuwa shekarar 2035 domin taimakawa matalautan kasashe.
An azawa wakilan gwamnatocin duniya a babban taron da aka gudanar a Baku, babban birnin Azerbaijan, nauyin amincewa da tsarin samar da makudan kudin domin fuskantar sauyin yanayi, to sai dai tattaunawar ta yi arangama da rarrabuwar kawuna tsakanin attajiran gwamnatoci dake turjiya ga yawan kudin, da cigaba da fargabar neman kari da ga kasashe masu tasowa.
Taron na makonni biyu a birnin dake kusa da ruwa, da aka kamala a yammacin Juma’a, sai da ya zarce lokacin da aka tsara za’a kammala shi, a dai dai lokacin da ake cigaba da gunaguni, tare da fatan cimma gurin tara kudin da aka shata na dala bilyan 250.
Wakilin musamman na kasar Panama ga taron sauyin yanayin, Juan Carlos Monterney Gomez, ya bayyana cikin fushi, yana cewa, ‘wannan abin takaici ne matuka,’ inda yace kudin da aka kiyasta tarawa ko kusa basu isa ba! Yace bisa ga dukkan alamu kasashen da su ka cigaba a duniya na son ganin duniya ta kone.
Wani mai shiga Tsakani daga Turai, tun da farko ya shaidawa kafar labaran Reuters cewa, adadin dake kunshe a jadawalin da shugabancin taron ya sanar yayi tsauri a yawa, kuma bai matsa kaimi ba sosai wajen fadada yawan kasashen da zasu samar da kudin.
Ya kara da cewa, ba wanda abin yayiwa dadi, saboda adadin yayi yawa matuka, sannan ba wata alamar kara yawan wadanda zasu samar da kudaden.
Kasashen da ake sa ran zasu jagoranci samar da kudin sun hada da, kungiyar tarayyar Turai, Austreliya, Amurka, Birtaniya, Japan, Norway, Canada, New Zealand da Switzerland.
Jadawalin tara kudin ya nemi kasashe masu tasowa da su bada gudummuwar abinda za su iya, tare da jaddada cewa, bayar da kudi ga batun sauyin yanayin ba zai shafi matsayin su ba na kasashe masu tasowa a Majalisar Dinkin Duniya, wani abu da ya shata jan layi ga kasashen da suka hada da China da Brazil.
Wakiliyar Jamus a wurin taron Jennifer Morgan tace, ba a kai wurin ba tukuna, to amma akallah ba a makale a cikin iska ba game da batun.
Tattaunawar dai tayi tarnaki sakamakon rashin tabbas dangane da irin rawar da Amurka za ta taka a yarjejeniyar, bayan da Donald Trump, wanda aka sani da wancakali da batun sauyin yanayi. Ya lashe zaben shugaban kasar Amurka ne a ranar 5 ga watan Nuwamba