Yace babbar fatarsu na 'yan Najeriya ita ce a samu a zauna lafiya a kasar tare da cigaba.
Sun yi addu'ar Allah ya ba shugaban kasa lafiya ya kuma taimakeshi ya sauke alkawarin da ya yiwa 'yan Najeriya. Ya kira 'yan Najeriya daga koina su cigaba da yin addu'o'i ma shugaban kasa da ma kasar domin samu cigaba.
Yau da azumi ke cika ishirin da tara za'a fara duba watan shawal na karamar sallah.
Kwamishanan 'yansandan Abuja Usman Alkali Baba ya zauna da limaman masallatan idi da kungiyar farar hula masu hulda da 'yansanda domin tabbatar da tsaro a filayen idi.
Yace sun san matakan da suke dauka wadanda ana ganin kamar musgunawa mutane ne musamman idan aka ce a ajiye mota a wani wuri ko a yi wani abu. Yace sun yi tanadin yadda zasu lura da ababen hawa da za'a ajiye. Saboda haka ya kira jama'a su dinga basu hadin kai domin duk abun da su keyi domin jin dadin jama'a ne.
Taron idi ya sha banban da sallar juma'a inji Malam Usaini Zakariya wanda ya kira a hada kai da jami'an tsaro a lokacin sallar idi domin samun masalaha, yansanda kuma su kawo doki domin wuri ne budadde.
Alhaji Sabo Keffi na nasihar cigaba da ayyukan alheri da adalci kan kowa. Yace jajircewar shugaban kasa Muhammad Buhari kan yaki da cin hanci da rashawa da tabbatar da gaskiya yana da kyau kuma ya kirashi ya cigaba da dagewa domin shi ne shirin zaman lafiya.Mabiya kuma su cigaba da hakuri su yadda zasu gyara.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5