An Kame Wasu ‘yan Adawa A Jamhuriyar Kamaru

  • Ladan Ayawa

Shugaban Kamaru, Paul Biya

Tun makon data gabata ne ‘yan adawan suka lashi takobin cewa a duk jumaa zasu yi zanga-zanga ta lumana.

Kuma a duk ranar da zasu yi zanga-zangar zasu sanya bakake kaya, ranar da suka kira ta bakar jumaa.

A ranar Jumaan data gabata a unguwar da ake kira akasiwa dake a birnin Yaounde, ‘yan adawan kusan su goma da suka hada da Kawala shugaban jamiyyar Cameroon Peoples Party da wasu tawagar’yan adawan aka kama su yayin da suke kokarin raba takardu wannan zanga-zangar.

Bayan an kama su ne aka tafi dasu barikin sojan kasar,

Ga Muhammadu Danda da ci gaban rahoton 1’17

Your browser doesn’t support HTML5

An Kame Wasu ‘yan Adawa A Jamhuriyar Kamaru 1'17