An Kame Wani Matashi Dangane Da Harbe Harben Da Akayi A Jihar Washington

An ki bayar da belin matashin nan dan shekaru 20 da haihuwa, wanda aka kama dangane da harbe-harben da aka yi.

An dai yi harbe harben ne a wani dandalin saye-da-sayarwa a jahar Washington ta arewa maso gabashin Amurka zuwa jiya Lahadi, kuma ya na fuskantar tuhumce-tuhumce guda biyar masu nasaba da laifin kisan kai na matakin farko, bisa ga bayanan gidan yari.

An damke Arcan Cetin na Oak Harbor, jahar Washington ranar Asabar, bayan kusan sa'o'i 24 da fara nemarsa ruwa a jallo. Da farko an yi kuskuren bayyana Cetin, wanda ya taho daga Turkiyya, cewa shi ba-hisfane ne, bayan harin.

Babban jami'in 'yan sandan Sintiri na jahar ta Washington Saja Mark Francis ya fadi jiya Lahadi cewa baya ga zuwa wani gida a Oak Harbor mai alaka da Cetin, masu bincike na kuma dudduba cikin motarsa ko za su gano wani abu mai alaka da abin da ya ingiza shi.

Jami'ai sun ce wani dansanda ne, wanda aka rada masa cewa Cetin na wuraren, ya je ya damke shi yayin da ya ke tafiya kan titi daura da gidansu da ke Oak Harbor a jahar ta Washington.

Da 'yansanda su ka tinkare shi, bai gudu ba, a cewar Laftana Mike Hawley na Ofishin babban jami'in 'yansandan Karamar Hukumar Island. A maimakon haka, sai ya saduda ya mika wuya, a cewar Hawley. Cetin bai dauke da wani makami a lokacin da aka kama shi.
An tsai da yau Litini don gurfanar da Cetin a kotu.