An Kama ‘Yan Jaridu Masu Zaman Kansu a Vietnam

White House

Amurka ta damu da batun Nguyen Thanh Nha, Doan Kien Giang, da Nguyen Phuoc Trung Bao, 'yan jarida uku masu zaman kansu da hukumomin Vietnam suka kama a ranar 20 ga Afrilu, da kuma abokin aikinsu, Truong Chau Huu Danh, wanda aka tsare a ƙarshen Disamba . Dukkaninsu an tuhume su ne a karkashin Mataki na 331 na Kundin Tsarin Mulkin Vietnam, wanda ya hana “cin zarafin demokraɗiyya don keta alfarmar Jiha”. Hukuncinzai kai ga ɗaurin shekaru 7a kurkuku.

Truong Chau Huu Danh na ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa, kuma mai ba da gudummawa ga, gidanuniyar labarai mai zaman kanta na Facebook, Bao Sach, ko " Tsabtaciyar Jarida ". A cewar Kwamitin Kungiya mai zaman kansa don Kare 'Yan Jarida, a lokacin da aka kama Danh a ranar 17 ga Disamba, 2020, Bao Sach na da mabiya sama da 100,000 a Facebook. Ya yi Magana akan batutuwa kamar cin hanci da rashawa da kuma sanya hotunan jami'an gwamnati da ake zargi da mu'amalar son kai. An rufe shafin Bao Sach na Facebook sakamakon kamun Danh.

"Wadannan kame-kamen 'yan jaridar su hudu kwanan nansu ne ba baya bayan nan a jerintsare-tsare da yanke hukuncin 'yan kasar Vietnam da ke amfani da hakkinsu na fadin albarkacin baki kamar yadda yake a cikin kundin tsarin mulkin Vietnam," a cewar Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Ned Price a cikin wata rubutacciyar sanarwa.

“Amurka na kira ga hukumomin Vietnam da su saki duk wadanda aka tsare bisa zalunci kuma su kyale dukkan mutane a Vietnam su bayyana ra’ayoyinsu ba tare da fargaba ba. Muna bukatan gwamnatin Vietnameseta tabbatar da ayyukanta sun yi daidai da tanadin haƙƙoƙin ɗan adam na kundin tsarin mulkin Vietnam da wajibanta na ƙasa da ƙasa, ”inji shi.

“'Yancin 'yan jarida na da mahimmaci ga tabbatar da gaskiya da rikon amana. Marubuta, masu rubutun ra'ayin yanar gizo, da 'yan jarida galibi suna yin ayyukansu cikin haɗari, kuma muna bukatan gwamnatoci da' yan ƙasa a duk duniya su tabbatar da kariyarsu. "