An Kama 'Yan Fashi Da 'Yan Damfara Masu Amfani Da Yanar Gizo a Nijer

An kama 'yan Damfara a Nijer

A jamhuriyar Nijer ‘yan sandan farin kaya sun kama wasu gaggan barayi da suka hada da ‘yan fashi da masu damfara ta yanar gizo

Rukuni na farko na barayin da ‘yan sanda suka gabatar wa manema labarai a ranar Alhamis 3 ga watan Satunba shine wanda ke kunshe da ‘yan fashi masu kai farmaki da rana kiri kiri a kamfanonin aika sakonnin kudade wato Agence de Transfert.

Jami’in hulda da jama’a Commissaire Abou Mountari, shine kakakin hukumar ‘yan sanda na kasa, ya ce an kama mutum 5 cikin gaggan barayin ana kuma neman wani. Ya kara da cewa kudi miliyan 23 da yan kai na CFA da kuma wayoyin hannu da kwamfuta aka sace a wani hari da barayin suka kai da bindiga.

Wani bakon al’amari da ‘yan sanda suka bankado shine na amfani da yara kanana domin zambatar bayin Allah a biranen Maradi da Yamai.

An Kama 'Yan Damfara a Nijer

Daga cikin wadanda dubunsu ta cika a wannan karon har da masu damfara ta hanyar yanar gizo wadanda suka yi nasarar kutsawa cikin manhajojin kamfanonin sadarwa na wayar tafi da gidanka.

A karshe ‘yan sanda sun gabatar da wani mutum da ya yi amfani da wannan lokaci na fama da annobar coronavirus don damfarar matasa masu neman aikin yi.

Hukumar ‘yan sanda ta gargadi jama’a su yi takatsantsan a wannan lokaci na yawaitar aiyukan ‘yan damfara da na ‘yan takife, sannan ta ja hankalin iyaye su kula da tarbiyyar yara.

Saurari cikakken rahoton Suley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kama 'Yan Fashi Da 'Yan Damfara Masu Amfani Da Yanar Gizo a Nijer