Kwanaki biyar bayan da sojojin Nijeriya su ka fara kai farmaki kan 'yan Boko Haran a Arewacin kasar hukumar sojin kasar ta ce an kama 'yan kungiyar 65 aka kashe kuma 10.
WASHINGTON, DC —
Kwanaki biyar bayan da sojojin Nijeriya su ka fara kai hare-hare kan 'yan kungiyar Boko Haram a Arewacin kasar, Ma'aikatar Tsaron kasar ta ce an kama 'yan kungiyar 65 aka kuma kashe guda 10; sannan kuma an kafa dokar fita ta sa'o'i 24 a sassan birnin Maiduguri a wuraren da ake kyautata zaton 'yan kungiyar na da tunga.
Ibrahim Alfa Ahmed, wanda ya shirya wannan rahoton, ya ruwaito wakiliyar Muryar Amurka Heather Murdock na cewa rundunar sojojin Nijeriya ta ce 'yan kungiyar ta Boko Haram na gudu daga sansanoninsu. Wasunsu sun bazu wurin neman man fetur ko dizil domin ababen hawansu yayin da kuma ke kokarin tsere wa sojojin da su ka far ma sonsanonin na su.
Wannan al'amarin ya biyo bayan dokar ta bacin da aka kafa don yakar 'yan kungiyar ta Boko Haram. A cikin sanarwar da ya bayar a yau Asabar, kakakin Ma'aikatar Tsaron Nijeriya, Birgediya-Janar Chris Olukolade ya ce sojoji na cigaba da gwabzawa da 'yan Boko Haram kuma za su farauto wadanda su ka gudu su ka buya. To saidai wasu masu lura da al'amuran yau da kullum na ganin irin matakan da sojojin ke daukawa ba lallai su haifar da da mai ido ba.