A firar da ya yi da manema labarai Mai Kanuri na Ijora Alhaji Mustapha Muhammad ya bayyana sunayen wadanda aka kama.
Mutanen sun hada da Ibrahim Ali, Abubakar Ahmed, Gogwai Kansilo, Ibrahim Muhammad, Bana Gana, Bulama Ali da Adam. Ranar Juma'ar da ta gabata aka kamasu.
An dai kama mutanen ne a wurare daban daban, a wuraren da suke samun mafaka musamman wuraren da ake samun 'yan arewacin Najeriya.
Adam daya daga cikin wadanda aka kama kuma shugabansu an kamashi ne a harabar wani Coci a boye a cikin wata kwantena.
Mai Kanuri yace suna da hakimai a kowane bangare a Legas. Da zara wani daga kauyensu ya isa Legas sai ya je wurin da hakiminsa yake idan kuma an gane dan Boko Haram ne sai a kamashi a kaiwa Mai Kanurin.
Mai Kanuri yace suna aikin ne da hadin gwuiwar jami'an tsaro kamar yadda wani dan asalin jihar Borno ya tabbatar. Malamin da baya son a fadi sunansa ya ce da gaske ne ana kama 'yan Boko Haram a Legas. Yace ko satin da ya wuce an kama kusan goma.
Tuni aka tasa keyar wadanda aka kama zuwa jihar Borno ga hannun rundunar tsaro dake yaki da kungiyar Boko Haram
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5