Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo, ta kama wasu masu satar mutane kuma ‘yan fashi da makami masu satar manyan motoci da lodin kayayyaki da dai sauransu.
Masu satar mutanen da manyan motoci shake da lodi dai sun fadi cewa sune suka aikata wannan danyen aikin a lokacin da kwamishinan ‘yan Sanda na jihar Oyo, Oyegbade, ya gabatar dasu ga manema labarai a hedikwatar ‘yan Sanda dake Eleyele a Ibadan.
Kwamishinan ‘yan Sandan ya kara da cewa ba zasu bar masu aikata laifuffuka ba su karbe jihar Oyo, ya ce suna da kwarararun jami’ai, da karfin hali da kwazon kawar da masu aikata laifuffukan.
Ya kara da cewa zasu tabbatar da ganin cewa jihar Oyo, ta zama jihar da bata da masu aikata danyan aiki, ya kuma bukaci duk masu halin kuruciyar bera da wasu miyagun halaye dasu san inda dare yayi masu.
Wanda aka sace a Gonarsa ya bayyana yarda aka sace shi ya ce yana Gonarsa a lokacin da mutane uku suka sameshi suka ce suna neman aikin gona yana kokarin ya yi masu bayyani cewa babu aikin gona sai suka damke shi suka rufe masa baki suka shiga daji dashi daga baya ‘yan uwansa suka shaidawa ‘yan sanda kana aka gano shi.
Makaman da aka samu a hannu masu satar mutanen sun hada da bindigogi da albarusai da adduna.
Your browser doesn’t support HTML5