A jiya Talata ne a ka kama wasu mutane guda biyar a kasar Jamus inda ake zarginsu da daukan mayakan kungiyar yan ta’adda ta Dae’sh. Ministan shari’a Heiko Mass ya kira kamen da “Sare gwiwa ga harkokin masu tsatstsauran ra’ayi a Jamus”.
WASHINGTON, DC —
Jami’ai sun bayyana cewa an kama wadanda ake zargin ne a bayan jerin samame da aka kai a wajen da ake kira Lower Saxony da Arewacin-Rhine jihar Westphalia. Ana tuhumar mutanen da shirya Kungiyar Jihadi da kuma kokarin daukan Musulmai zuwa Syria domin yaki tare da Yan tsagerun Da’esh.
Masu bincike sun bayyana daya daga cikin mutanen dan asalin kasar Iraqi mai shekaru 32 da akewa lakabi da Abu Walaa, a matsayin shugaban kungiyar. Rahotanni sun nuna sauran da ake zargi sun hada da Dan kasar Turkiya, Bajamushe, Dan Serbia da kuma Jamus tare da Dan kasar Kamaru.