Hukumomin kasar Kamaru sun tsare wadansu 'yan Najeriya guda talatin da suka ketara kan iyaka, ranar Asabar bisa tunanin suna da alaka da kungiyar Boko Haram.
'Yan sanda sun ce gungun mutanen wadanda galibi mata ne da kananan yara, basu nemi izinin ketara kan iyakar ba, basu kuma da katunan shaidar tantancewa, yayinda suka kasa amsa tamabayoyin da aka yi masu.
Jami'an tsaron kasar Kamaru sun ce sun hango motar safa dake dauke da mutanen, da aka tsare ne yayinda suke ketara kan iyakar daga Gamborou Ngala, inda kungiyar Boko Haram take da karfi a lokutan baya.
'Yan sanda a Maroua sunce suna gudanar da bincike domin tantance mutanen da kuma sanin dalilansu na shiga Kamaru.
Kawo yanzu, Hukumomin Najeriya basu maida martani dangane da tsare mutanen ba.