An kama wani mutum dake shirin kai harin ta'addanci a Washington, DC

Amine El Khalifi Amine a gaban alkali

Hukumomin kasar Amurka sun ce sun kama wani mutum kusa da ginin majalisar dokokin kasar wanda suka ce yana kokari ya kai harin ta’addanci.

Hukumomin kasar Amurka sun ce sun kama wani mutum kusa da ginin majalisar dokokin kasar wanda suka ce yana kokari ya kai harin ta’addanci.

Jami’an tsaro sun ce mutumin dan shekaru 29 da haihuwa dan asalin kasar Morocco ya yi kokarin amfani da abinda ya zaci nakiyoyi ne ya kai hari a majalisar. Suka kuma bayyana cewa, jami’an tsaro sun warware nakiyoyi yadda ba zasu iya tashi ba kuma basu da wani hadari ga al’umma.

Yan sandan majalisar sun ce ana tsare da mutumin mai suna Amine El Khalifi ne a cikin wani bincike mai tsawo kuma cikakke da ‘yan sandan ciki na FBI suka gudanar.

Ma’aikatar shari’a ta Amurka tace Khalifa ya yi bayyanar farko gaban alkalin tarayya jiya jumma’a aka kuma tuhume shi da laifin yunkurin amfani da makaman kare dangi.

Ma’aikatar tace da farko Khalifi ya yi shirin kai hare hare a wurare da dama da suka hada da cibiyoyin rundunar soji da gidajen cin abinci da kuma wata masujada ta Yahudawa.

Rahotanni na nuni da cewa Khalifi yana Amurka ne ba tare da izini ba kuma bashi da alaka da kungiyar al-Qaida.

An kama mutumin ne kwana daya bayanda aka yankewa wani dan Najeriya hukumcin daurin rai da rai a Amurka sabili da kokarin tarwatsa wani jirgin saman sufuri na Amurka wanda ya tashi daga Amsterdam zuwa Amurka ranar Kirsimeti shekara ta dubu biyu da tara da nakiya da ya boye a kamfanshi. Jami’an Amurka sun dora alhakin yunkurin kai harin na Umar Farouk Abdulmutallab kan kungiyar al-Qaida ta Yemen.