An Kama Wani Matashi Mai Lalata Da Dabbobi

Akuya

An kama wani matashi dan kasar Kenya, mai shekaru ashirin da ukku, da haihuwa mai suna Otieno Jalango, da laifin yin lalata da Akuya.

An kamashi ne a kudu maso gabashin Muhuru, a yankin Nyatike dake karamar hukumar Migori, a kasar Kenya, yana aikata wanna tu’annati da dabar.

Da aka kama shi matashi, ya amsa laifinsa da cewa ya dade yana aikata hakkan dalilinsa shine wai yana gudun kamuwa da cutar kanjamau daga mata shi yasa yake lalata da dabba.

Hakimin yankin Jim Kawa, yace mazauna yankin ne suka mika shi kareshi suna masu cerwa sun damu matuka da batun dabbobinsu saboda wannan dabiyar ta jalango.

Hakimin, ya kara da cewa Jalango, yace ya kanyi lalata da dabbobi kamar Tikiyoyi, jakai da Karnuka.